Habasha Da Somaliya Sun Tattaunawa Hanyoyin Sake Mayar Da Alaka

Fira ministan hakar Habasha  Abiy Ahmed ya sami kyakkyawar tarba daga shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mamhud a birnin Mogadishu na Habasa a ranar Alhamis

Fira ministan hakar Habasha  Abiy Ahmed ya sami kyakkyawar tarba daga shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mamhud a birnin Mogadishu na Habasa a ranar Alhamis da ya kai ziyara domin bunkasa alaka a tsakainin kasashen biyu.

Sabani a tsakanin kasashen biyu masu makwabtaka da juna ya kunno kai ne a shekarar da ta gabata, bayan da kasar ta Habasha ya kulla yarjejeniya da yankin Somaliland akan tashar jirgin ruwa.

Ita dai kasar ta Habasha ba ta da iyaka da ruwa, don haka take son amfani da mashigar ruwan kasar ta yankin Somaliland. Habashan dai tana son gina wani yanki na kasuwanci a gabar ruwan  ta yankin Somaliland.

 Yankin Somaliland na kasar Somaliya ne wanda Mogadishu  take daukar cewa ba kasa ce mai cin gashin kanta.

Somaliya ta nuna fushinta akan waccan yarjejeniyar tare da zargin Habasha da yin kuste a cikin iyakokin kasarta.

A cikin watan Disamba ne dai Turkiya ta fara shiga tsakanin kasashen biyu domin  warware sabanin da yake a tsakaninsu.

Tattaunawar ranar Alhamis din a tsakanin kasashen biyu ta mayar da hankali ne akan kasuwanci, da tsaro da kuma batun sake mayar da alakar da diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments