Hukumar abinci ta duniya ( FAO) ta sanar da cewa bisa la’akari da yadda adadin mutanen Afirka yake karuwa da kaso 2.3% a kowace shekara, hakan yana nufin cewa amfani da alkama zai karu.
Bugu da kari hukumar abincin ta duniya ta ce da akwai wasu dalilan da za su sa Rashan ta kara yawan kai alkamar zuwa nahiyar Afirka da su ne fari da ake fama da shi Arewacin Afirka da kuma ambaliyar ruwan sama a yankin Sahel.