17-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, barkammu da sake saduwa cikin shirimmu na Al-adu da ci gaban addinin musulunci a tarihi, shirin da ke kawo muku irin ciki gaban da addinin musulunci da musulmi suka samu tun bayan bayyanarsa zuwa yau, wanda ni Tahir Amin nake kawo muku sau guda a ko wane mako. Da fatan masu sauroro zasu kasance tare da mu a wanan makon.
///…Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu, a cikin shirimmu da ya gabata, mun yi maganar yanda massalatai suka ci gaba da zama cibiyoyin yada al-adu da ci gaban addinin musulunci, tun bayan hijirar manzon All..(s) har zuwa yau. Masallatai suna na farko kuma sun ci gaba da kasancewa hakan har zuwa yanzun.
Mun bayyana cewa, banda manya manyan makarantu da aka samar daga baya, da dakunan karatu da wasu cibiyoyin yada ilmi, a kasashen musulmi, masallatai sun ci gaba da zama ciyar yada ilmi da al-adun addinin musulunci har yanzun, kuma a halin yanzu an fi yada tarbiyya da kuma tunatarwa ga musulmi don kusanto da su zuwa ga ubangijinsu.
Mun bayyana cewa akwai wasu masallatai a wasu kasashen musulmi tun lokacinda aka gina su, shekaru fiye da dubu guda da suka gabata, suna nan a matsayin cibiyar yada ilmi da al-adun musulunci. Mun ambaci wasu masallatai wadanda suka hada da tsohon masallaci na birnin Nishabur a yankin Khurasan na kasar Iran da masallacin Akilu, da masallacin manzon All..(s) a Madina, da masallacin Kufa da sauransu.
Wadannan masallatan sun fi shekaru 1000 a duniya, basu sauya matsayinsu ba na zama cibiyoyin yada al-adu da ci gaban addinin musulunci ba. Mun bayyana cewa, bayan manzon All..(s), Imam Ali (a) Amirulmuminina (a) da dansa Imam Al-Hassan, da Hussain da sauran Limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s) sun ci gaba da wannan tsarin ta maida masallaci cibiyar yada al-adu da ci gaban addinin musulunci.
Mun bayyana cewa Limami na 6 Imam Jaafar dan Mohammad Assadik (a) yana da dalibai kimani 4000 a cikin al-ummar musulmi, sannan ya koyawa da dama daga cikinsu wasu fannonin ilmi, na rayuwa ba na ilmin ba, da kuma na addinin.
Ya koyawa Jabir dan Hayyan ilmin kimiyyar lissafi wato Chemistry, da wannan dalolin ne jabir ya zama mutum na farko wanda ya samarda sulfuric Acid, ko muce tsami. Sai Hisham dan Hakam a ilmin akidu da sanin All.., da kuma Aban dan Taglib a ilmin fikihu da sauransu.
Banda masallatai, kusa da kowannensu akwai dakunan karatu ko ajiyan littafai. Da wuya ka sami daya daga cikin manya manyan masallatai wadanda babu wurin ajiyar littafai kusa da su ba.
Masallatai kamar masallacin Al-Aksa, a kasar Falasdinu, masallacin umayyawa a Dimash, masallaci babban a birnin Tunis, Jami’ar Al-Azhar a birnin Alkahira, da Jami’ar Zaitun ta Tunisia wadan nan masallatai ko cibiyoyin karatu suna da dakunan ajiyar littafai kusa da su.
Kuma a mafi yawan wurare masu tsarki a kasashen musulmi ana samun dakunan karatu manya manyan, kamar Haramin Makka ko ka’aba, (wato masjidul Haram), haramin manzon All..(s) a madina, Haramin Imam Ali (a) a Najaf, Haramin Musa dan Jaafaru (a) a bagadaza, da Haramin Imam Aliyu dan Musa Arridha(a) a birnin Mashad. Duk suna da dakunan ajiyar Littafai.
Haka ma kusa da kaburburan waliyyan All..wadanda suka hada da Maulana, a Quniyeh, a kasar Turkiyya. Mazar Gazan-Khan a Tabriz da mazar Sheikh Ahmad Jam a Turbat Jam suma suna da dakunan ajiyar littafai masu girma.
A wani bangare akwai wasu asbitoci a cikin kasashen musulmi wadanda aka gina dakunan ajiyar littafai don amfanin likitoci, don gudanar da bincike da kuma karin karatu dangane da cututtuka da hanyoyin jinyar marasa lafiya. Daga cikin wadannan asbitoci a kwai Asbitin Fustaad (fusat) a kasar Masar, asbitin babba na Mansuri a cikin birnin Alkahira shi ma a kasar Masar. Sai asbitin Mktadir a cikin birnin Bagdaza, da asbitin Ray a kusa da birnin Tehran a kasar Iran.
Sai kuma sauran cibiyoyin yada ilmi da al-adun addinin musulunci, a makarantu. Makarantu ma suna da dakunan ajiyar littafai, kusa ko kuma cikin ko wace makaranta, a inda malamai da dalibai suke zuwa don bincike da kuma fadada ilminsu a lokaci ko bayan karatu.
Muna iya cewa da wuya ka sami makarantar da bata da dakin ajiyar Littafai a kasashen musulmi a lokacin har zuwa yanzu. Makarantun da suka shahara kuma suke da dakunan ajiyar littafai a kasashen musulmi suna da yawa, kuma sun hada da Makarantar Nizamiyya ta Bagdaza, Makarantun Shamisadiyya da Khusrawiyya a birnin Dameshq na kasar Siriya. Makarantun Halawiyyah da Sharafiyya a birnin Halab, da makarantar Sultania a birnin Al-Kahira da wasu daruruwan makarantu, duk suna da dakunan karatu a kusa da su ko cikinsu.
Banda wadannan, muna da wasu dakunan karatu ko ajiyar Littafai masu zaman kansu, ba kusa da masallatai ba kuma kusa da makarantu da cibiyoyin ilmi ba. Kuma sun hada da Darul Ilmi, darul Kutub, da Khazanatul Hikma a kasashe daban daban aduniya musulmi.
Wadannan dakunan ajiyar Littafai, a lokacin ko kuma har yanzun dama wurare bincike da karatu ko wallafe wallafen littafai ne da kuma tarjama. Kuma irin wadannan dakunan ajiyar Littafan sun hada da Khazanatul ilmi wanda Aliyu dan Yahya Munajjim ya gina.
Wannan saboda a lokacinda aka fara yunkurin tarjamah, tare da shi akwai ayyukan wallafe wallafen littafai.
A dai dai lokacinda ake fatahin kasashe wadanda ba musulmi ba, ana kuma samun littafai wadanda aka yi ganimarsu zuwa wadannan cibiyoyin tarjama, hakama aikin wallafe wallafe suka yunkura tare da su. Wannan yanayin ya samar da dakunan ajiyar littafai a manya manya birane da kanana a dukkan kasashen musulmi.
Wasu Malaman tarihi sun bayyana cewa, mafi yawan wadannan dakunan ajiyar littafai masu zaman kansu, wadanda kuma aka fara samarda su a farkon karni na 4 kamariyya, an samar da su ne da sunan wakafi, kamar yanda addiniyar musulunci ya kwadaitar da samar da abubuwa masu amfani wadanda har bayan mutuwar wanda ya samar da shi zai ci gaba da samun ladansa, har zuwa gushewarsa.
Don haka masu hali da dama sukan gina dakunan littafai su bari a bayansu, don su ci gaba da samun lada har bayan mutuwarsu, ana kiransa ‘sadakatul Jariya. Sadaka mai gudana, wato mai samar da lada mai gudana har bayan mutuwa. Ko kuma wanda aka fi saninsa da wakafi.
Daya daga cikin wadannan dakunan ajiyar littafai ko cibiyoyin yada ilmi, sun hada da Darul Ilmi na fadimawa wanda aka samar da shi a shekara ta 395 K. a birnin Al-Kahira na kasar Masar. Ana karantar da ilmin lissafi, ilmin dabi’a, da sauransu a wannan cibiyar, sannan an samar da dakin ajiyar littafai mai mujalladi kimani miliyon guda a cikinsa.
Sai kuma Darul Ilmi na Musil yana da wani dakin ajiyar littafai sanennen mai kuma girma. A cikin wannan dakin ajiyar littafai da jama’a, an tattara littafai daga ko wani fannin ilmi.
Darul Ilmi na Tarabulus, Bagdaza da Qudus da sauransu suna dauke da dubban daruruwan littafai. Sannan malamai da masu bincike da mawallafa da dama suka amfana da su.
Daga cikin cibiyoyin yada ilmi da al-adun musulunci a cikin tarihin addinin musulunci, sun hada da makarantun Nizamiya. A rabin karni na 5 hijira Khoja Nizamul mulki minister sarki Alib Irsaalaan salujuqawa ya kafa makarantu masu kama da Jami’o’ii wadanda ya kira Nizamiyya a Bagdaza da Nishabur da wasu birane da dama a lokacin.
Khoja Nizamul Mulki ya daga wannan nau’in cibiyoyin ilmi a cikin al-adu da ci gaban addin musulunci a tarihi a marhala mafi kolinsa. An kafa makarantar Nizamiya na Bagdaza ne a shekara ta 459 K. Wanda kuma shi ne, makaranta mafi koli a marhalolin karatu a duniyar musulmi a lokacin, ta sami halattar Abu Ishak Shirazi wani babban malami a zamanin a matsayin mai karantarwa a cikinta.
Banda haka daga baya Imam Al-ghazali mai littafin Ihyau Ulumuddin ya zama malami a makarantar na wani lokaci. Daga nan ne irin wadannan makarantu ko cibiyoyin ilmi mai zurfi suka fara yaduwa a cikin kasashen musulmi.
A lokacin dakin littafai na karatu a Nazamiyah a Bagdaza ya zama dakin ajiyar littafai ko karatu mafi girma a jami’o’in kasar.
Nazamul Mulki ne ya gina wannan dakin karatu, kuma shi da kansa ne ya kula da yanda aka gina shit un farko har aka kammala. Ga wanda yake son karin bayani zai iya samun tarihin wannan dakin ajiyar littafai wanda aka rubuta.
Wani abin lura a nan shi ne, ana kiran wadanan cibiyoyin karatu da kuma dakunan karatu da Nizamiyyah ne, saboda shi Nazamul Mulki ne ya gina su a zamanin sarakunan Salujukawa.
Don haka Nizamiyya ta Bagdaza tana da babban fili, mai fadi, tare da manya manyan gidajen malamai da masu karantarwa, da babban masallaci da kuma dakin ajiyar Littafai.
Kuma saboda tsare-tsaren tattaunawa da maganganu masu fadi da zurfi dangane da addini wanda wannan makarantar Nizamiyya take da shi, ta shahara a cikin dukkan kasashen musulmi.