Adai dai lokacin da ke ta tattaunawa tsakanin Amurka da Indiya kan harkokin kasuwancin , sai ga shi a makon da ya wuce New Delhi ta karbi bakunci daya daga cikin manyan shuwagabannin dake kalubalantar gwamnatin Amurka akan nuna fin karfin a duniya.
Shugaban kasar Rasha viladmir Putin ya kwashe kwanaki biyu a indiya a wata ziyarar aiki da ya kai, kuma wannan yana zuwa ne adaidai lokacin da indiya ke fuskantar harajin da Amurka ta sanya mata na kashi 25 cikin 100 saboda ci gaba da siyan mai a hannun kasar Rasha , lamarin da ya kawo tarnaki a alakar dake tsakanin Delhi da kuma Washinton.
Bugu da kari Amurka ta sanar da takunkumin ne a ranar 23 ga watan oktoba akan manyan kamfanonin mai na kasar Rasha da hakan ha haifar da barazana ga kasar indiya dake neman shigo da man fetur mai sauki daga rasha, sai dai rahotanni sun nuna cewa har yanzu dai kasar indiya itace babbar mai sayan manfetur din kasar Rasha.
Tun a shekara ta 1960 Mosko da New Delhi ke da kyakkayawar dangantaka ta kud da kud da ya hada da kasuwancin , hadin guiwar Soja , kimiyya ,makamashi da kuma sararin samaniya.