Dakarun kare juyin juya halin musulunci bangare sararin samania sun bada labarin arcewar jirgin yakin Amurka samfurin F-16 daga sararin samaniyar mashigar ruwa ta Hurmuz bayan harbin gargdi da suka yi masa.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar ya nakalto majiyar IRGC na fadar haka a wata sanarwan da suka fitar a safiyar yau Jumma’a. Sanarwan ta kara da cewa, jirin yakin ya tunkariya saman mashigar ruwa ta Hurmuz daga kudu masu gabacin yankin, a wani shiri na rikiyar wasu jiragen ruwa dauke da mai wucewa ta hanyar da Iran ta haramta daga kudancin mashigar ruwa ta Hurmuz.
Jirgin ya gamu da wani harbin gargadi mai karfi daga tsarkin garkuwan sararin samaniya na sojojin kasar, wanda ya tilasta masa, sauya hanyarsa ya nisantar da kansa daga saririn samaniyar kasar Iran.
IRGC sun kara da cewa, Iran ba zasu amince da sace hanyar wucewa da mashigar ruwa ta Hurmuz ba, kuma duk wadanda suka yi kokarin haka zasu gamu da fushinsu.
Sun kara da cewa sararin samaniyar kasar Iran ya haramta ga sojojin Amurka, kuma jan layi ne ga Iran Iran duk wanda ya tsallaka wannan layin zai ji ba dadi.