Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya mika ta’aziyyar Iran ga iyalan wadanda gobara ta shafa a kasar Masar
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran Isma’il Baqa’i ya aike da sakon ta’aziyyar al’umma da gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma gwamnati da al’ummar Masar.
A cewar kamfanin dillancin labaran Mehr, bayan tashin gobarar sanadiyyar kifewar wata tankar mai ta kuma kama da wuta a gudumar Giza da ke kasar Masar, wadda ta yi sanadiyyar mutuwan mutane sama da 50.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar ta Iran ya bayyana ta’aziyyar al’umma da gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma gwamnati da al’ummar Masar. Yana addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya ba iyalan da suka rasa ‘yan uwansu hakuri da kuma samun lafiya ga wadanda suka samu raunuka tare da murmurewa cikin sauri.