Korea Ta Kudu: Babu Shiri Kai Sojojin Kasar Zuwa Yammacin Asia

Ministan harkokin wajen kasar Korea ta Kudu Cho Hyun ya bayyana cewa gwamnatinsa bata da wani shiri na aika sojoji zuwa yankin yammacin Asia don

Ministan harkokin wajen kasar Korea ta Kudu Cho Hyun ya bayyana cewa gwamnatinsa bata da wani shiri na aika sojoji zuwa yankin yammacin Asia don taimakawa kasashen Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila (HKI) a yakin da take fafatawa da Iran.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a zantawarsa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Iran Abbas Aragchi. Kafin haka Abbas Aragchi ne ya kira Cho Hyun inda suka tattauna da farko kan dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma al-amuran da suka shafin yankin da kuma duniya gaba daya.

Daga nan Aragchi ya ce, aika da sojoji zuwa yankin yammacin Asia ba zai taimakawa zaman lafiya ayankin ba. Kuma zai kara lalata al-amura ne kawai.

Manya manyan Jami’an diblomasiyyar kasashen biyu sun tattauna kan kokarin da Iran da kasashen duniya suke yin a kawo karshen yakin ta hanyar Diblomasiyya da kuma dawo da zaman lafiya a yankin da kuma duniya.

Hyun ya bayyana gurinsa na garin an dawo da zaman lafiya da nutsuwa a yankin yammacin Asia, sannan bata da wani shiri na sanya kanta cikin rikicin. Yana kuma fatan za’a warwareshi ta hanyar diblomasiyya da tattaunawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted