Najeriya: An SaKe Fadawa Cikin Tashin Hankali A jihar Palateau

Akalla mutane 40 ne aka tabbatar da mutuwarsu a tashe tashen hankula na baya bayan nan a jihar Palateau na tarayyar Najeriya. Jaridar Daily Trust

Akalla mutane 40 ne aka tabbatar da mutuwarsu a tashe tashen hankula na baya bayan nan a jihar Palateau na tarayyar Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta bayyana cewa akalla mutane 40 ne suka rasa rayukansu, kuma sun hada da mata da yara da jami’an tsaro, wasu da dama sun ji rauni,  a tashe tashen hankula na kimani makonni 3 da suka gabata.

Labarin ya kara da cewa an kona gidaje da dama sannan an sace shanu kimani 100. Sannan yankunan da abin ya shyafa sun hada da  Bassa, Barkin Ladi, Riyom, Mangu, Bokkos da kuma karamar hukumar Qua’an Pan.

A wannan tashe tashen hankula bangarorin makiya da manoma duk sun yi asarar rayuka da dukiyoyi.

Labarin ya kara da cewa a ranar laraba ce aka fara rikcin a lokacinda wani dan bindiga ya bude wuta kan wasu mutane a cikin dare a garin Tafi Gana, da wani kauye da ake kira Kyie Ihwien kusa da Jebbu Miango a karamar hukumar  Bassa ya kashe akalla mutane 17, inji majiyar yansanda. Wasu sun ce adadin yakai 19 don mutane biyu sun mutu a asbiti.

Bangarorin biyu suna zargin juna da fara tashin hankalin, kungiyar Fulani makiyaya a yankin sun bayyana cewa jita jitan da ake yadawa dangane da sub a gaskiya bane. A wani bangaren kuma kungiyar matasan birom ta fitar da wani bayani inda take aza laifin tashe tashen hankula da baya bayan na kan kabilar Fulani makiyaya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted