Amurka Ta Bukaci Isra’ila Da Ta Tattauna Da Kungiyar Hamas

Wakili na musamman na shugaban Amurka ya ce: Dole ne Isra’ila ta yi watsi da tunaninta na yaƙi na dindindin ta kuma yi shawarwari da

Wakili na musamman na shugaban Amurka ya ce: Dole ne Isra’ila ta yi watsi da tunaninta na yaƙi na dindindin ta kuma yi shawarwari da kungiyar Hamas

Jared Kushner, wakili na musamman na shugaban Amurka, ya Jaddada cewa: Kawo karshen yaki a yankin Gaza yana bukatar tattaunawa da kungiyar Hamas, yana mai kira ga Haramtacciyar Kasar Isra’ila da ta yi watsi da ra’ayinta na yaki na dindindin ta kuma mai da hankali kan diflomasiyyar tattalin arziki. Ya amince cewa: Fira Ministan rikon kwarya Benjamin Netanyahu yana ci gaba da kawo cikas ga fahimtar juna game da yankin.

A cikin wata hira da kafar watsa labaran Jamus mai suna “MD Metz,” Kushner ya bayyana cewa: Amurka ta yi nasarar cimma yarjejeniya kan Gaza duk da cewa “da alama ba zai yiwu ba,” yana mai jaddada ci gaba da neman mafita duk da sukar da Isra’ila ke yi wa Hamas kai tsaye.

Ya lura cewa Amurka tana tattaunawa mai kyau da Netanyahu, inda ya ƙara da cewa, “Yana ganin ya fahimci muhimmancin shirin zaman lafiya na Gaza.”

Wakilin Amurka ya bayyana cewa Netanyahu ya sanya hannu kan yarjejeniyar Gaza, amma har yanzu yana sa ta zama da wahala a cimma fahimtar juna kan aiwatar da ita.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted