Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa tattaunawa tsakanin Iran da masu shiga Tsakani don kawo karshen yakin da Amurka da haramtacciyar kasar Israeil suka dorawa kasar na ci gaba.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Aragchi yana fadar haka,a jiya Alahamis, ya kuma kara da cewa, masu shiga tsakani,Qatar da Pakistan sun ci gaba da gabatar da shawarori dangane da yadda za’a kawo karshen yakin, kuma suna musayar ra’ayi da bangaren Iran ta majalisar koli ta tsaron kasar.
Ministan ya kara da cewa abinda ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta sanya a gaba a wannan lokacin shi ne tabbatar da cewa ta samarwa kasar garkuwa daga takurawar da makiya suke wa kasar ko ta ina.
Ya ce jami’an diblomasiyyar kasar Iran, musamman wadanda suke aiki a kan iyakokin kasar suna kokarin ganin hanyoyin shigo da kayaki cikin kasar Iran daga kasashe makobta sun ci gaba da kasancewa a bude, sannan sun kuma aiki tukuru don ganin kayakin da mutanen kasar Iran suke bukata matuka sun ci gaba da shigowa kasar duk tare da barazanar makiya na hanasu shiga kasar Iran har sai ta mika kai ga bukatunta.
Aragchi ya kara da cewa, muna son mu nuna wa kasar Amurka kan cewa bata isa ta rufe kan iykokin kasar Iran da makobtanta ba. Bata isa ta hana shigowar abinci da kuma kayakin da mutanen kasar Iran miliyon kimani 90 suke bukata ba.
Yace har yanzun kofar diblomasiyya a bude take, amma kuma suna aiki don ganin makiya basu kaiga bukatusu kan kasar ba, ta amfani da takunkuman tattalin arziki ko kuma amfani da makami.
Daga karshen ya ce majalisar koli ta tsaron kasar Iran ce take tattaunawa dukkan sabbin shawarorin da kasashen Qatar da Pakistan suka gabatar na dawo da zaman lafiya da kuma tabbatar da adalci ga Jumhuriyar Musulunci ta Iran.