Zarif: Sake Kakaba Wa Iran Takunkumi Ba Zai Amfani Kasashen Turai Ba

Tsohon ministan harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran, Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, har yanzu da akwai damar amfani da hanyoyin diplomasiyya domin warware

Tsohon ministan harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran, Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, har yanzu da akwai damar amfani da hanyoyin diplomasiyya domin warware batun Shirin Iran na makamashin Nukiliya da su ka hada da kafa wata cibiya ta tace uranium, da kuma sake sabunta hanyoyin aiki tare da hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa.

Tsohon ministan harkokin wajen na Iran ya kuma kara da hanyoyin na diplomasiyya sun kunshi sake bude tattaunawa da kasashen turai uku, da kuma Rasha da China, kuma watakila Amurka ta shigo daga baya. Sai dai kuma minstan harkokin wajen na Iran ya kara da cewa, sharadin samun nasarar ta fuskar diplomasiyya ya ta’allaka da idan kasashen turai sun daina halinsu na fuska biyu.

Muhammad Jawad Zarif ya kuma ce,bai san abinda kasashen turai suke son cimmawa ba,amma sakamanon da za su girba shi ne su fice daga zama abokan tattaunawa.

Bugu da kari, Muhammad Jawad Zarif ya ce, kasashen na turai sun yi wa Iran wasu alkawulla 11 da ba su yi aiki da ko da guda daya daga cikinsu ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments