Sojojin Isra’ila Sun Kashe Sama Da Falasdinawa 77 A Gaza A Yau Kawai.

Rahotanni sun bayyana cewa sama da mautane 77 su ne suka mutu a wani hari da HKI ta kai a yankin gaza a yau kawai, da ya hada da wani harin da takai da ya kashe mutane 11 iyalan mutum guda, Ma’aikatar lafiya ta bada rahoton cewa a ranar alhamis da ta gabata kimanin  falasdinawa […]

An Gudanar Da Taron Cika Shekara 1 Da Shahadar  Sayyid Nasrullah

Da yake bayani a wajen taron na tunawa da shahadar sayyid Hassan Nasrullah da kuma sayyid hashim safiyyudden , babban sakatare janar din kungiyar Hizbullah, shaikh Naim qasem,yace tsayin daka da marigayi sayyid hassan nasrullah  yayi ya zarce bangaranci, kuma ya zaburar da musulmi da kirsitoci da duk masu kishin addini , Yace tunani da […]

Yunkurin Jinkirta Dawo Da Takunkumi Kan Kasar Iran Bai Yi Nasara ba.

kwamtin tsaro

Yunkurin kasashen rasha da china na jirkinta dawowa da iran takunkumi har na tsawon wata 6 bai yi nasara ba a kwamitin tsaro na MDD saboda kasashe 4 ne suka nuna goyon bayansu da suka hada da kasashen China Rasha Pakistan da kuma Aljeriya, yayin da kasashe 9 kuma suka nuna rashin amincewa da shirin […]

Shugaban Hukumar IAEA Ya Ce Shirin Nukiliyar Iran Na Zaman Lafiya Ne

  Rafael Grossi babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA a wata hira da yayi da gidan talbijin din Russia 24 ya bayyana cewa shirin nukiliya iran na zaman lafiya ne baki daya. Wannan maganar ta yi karo da kalaman prime minister isra’ila Benjamin Natanyaho  inda ya nuna cewa shirin nukiliyar Iran babban […]

Shugaban Majalisar Tsaron Kasar Iran  Dr Ali Larijani  Ya Isa Birnin Berut .

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban majalisar tsaro na kasar iran Dr Ali larijani ya isa birnin berut na kasar labanon, kuma ya gana da shugaban majalisar dokokin kasar Nabi birri  ya kuma bayyana ta a matsayin mai amfani sosai domin ta mayar da hankali kan yadda zaa kara kyautata alaka tsakani. Haka zalika larijani ya […]

Iran ta kira jakadunta daga Birtaniya, Faransa, da Jamus domin tuntuba

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta kirayi jakadun kasarta a kasashen Biritaniya, faransa da kuma jamus domin tuntuba, a daidai lokacin da takun tsaka tsakaninta da kasashen ke kara kamari sanadin yunkuinsu na ganin an sake dawo ma Iran da takunkuman MDD. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar yau Asabar ta ce “Bayan matakin […]

MDD : Isra’ila na kai harin bam a Gaza kowane minti 8 ko 9

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin mummunan lamari ga fararen hula a Gaza yayin da sojojin Isra’ila suka tsananta kai hare-hare ta sama kan yankin da aka yi wa kawanya. Da yake ambato ofishin kula da ayyukan jin kai na OCHA, kakakin MDD Stephane Dujarric, ya shaidawa manema labarai cewa “Sojojin Isra’ila sun zafafa kai […]

MSF ta dakatar da ayyukan birnin Gaza saboda hare-haren Isra’ila

Kungiyar agaji ta Doctors Without Borders (MSF) ta ce an tilasta mata dakatar da aikinta a birnin Gaza saboda hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaiwa a Zirin. “Ba a ba mu wani zabi ba illa mu dakatar da ayyukanmu yayin da sojojin Isra’ila ke kewaye da asibitocinmu,” in ji Jacob Granger, jami’in agajin […]

Amurka Tana Shirin Kai Wa Venezuela Hari

Tashar talabijin din “NBC” ta Amurka ta bayar da labarin cewa gwamnatin Amurka tana Shirin kai harin soja akan wasu wurare a cikin kasar Venezuela. Tashar talabijin din na NBC ta ambato wasu majiyoyi 4 na Amurka da su ka bayyana cewa shugaban kasar Donald Trump bai kai ga bayar da umarnin kai harin ba, […]

 Zarif: Sake Kakaba Wa Iran Takunkumi Ba Zai Amfani Kasashen Turai Ba

Tsohon ministan harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran, Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, har yanzu da akwai damar amfani da hanyoyin diplomasiyya domin warware batun Shirin Iran na makamashin Nukiliya da su ka hada da kafa wata cibiya ta tace uranium, da kuma sake sabunta hanyoyin aiki tare da hukumar makamashin Nukiliya ta kasa […]

MDD Ta Kara Yawan Kamfanonin Da Suke Taimakawa HKI A Laifukan Yaki Zuwa 68

MDD ta kara yawan sunayen kamfanonin da su ka yi aiki tare da HKI wajen keta hakkokin al’ummar Falasdinu, ta hanyar ayyukan da suke aiwatarwa a cikin sansanonin yahudawa ‘yan share wuri zauna. A cikin rumbun bayanan MDD dai an fara zayyana sunayen  kamfanoni  11, da a halin yanzu sun karu zuwa 158. Tun a […]

Najeriya: Mutane Da Dama Sun Rasa Rayukansu A Wuraren Hako Zinariya

Rahotanni da suke fitowa daga Jahar Zamfara a arewacin Nigeria sun ce, mutanen da sun karaci 100 ake fargabar mutuwarsu saboda  ruftawar ramin hako ma’adanai. Shedun ganin ido sun fada wa kamfanin dillancin labarun “Reuters” cewa; ramin hako ma’adanan wanda yake a yankin Kaduri dake karamar hukumar Maru ya fada akan ma’aikatan dake ciki. Lamarin […]