Mataimakin shugaban kasar Iran mai kula da tsare-tsare dabaru Muhammad Javad Zarif ya ce Iran ba barazana ce ba ga tsaron wata kasa.
Zarif ya bayanna hakan ne a wata hira da tashar CNN a taron tattalin arzikin duniya karo na 55 a Davos.
‘’Ina Mai sake nanata cewa Iran ba ta da niyyar kera makaman kare dangi’’kuma da a ce Iran na son kera makaman nukiliya da tuni ta yi hakan.
“Ana kera makaman nukiliya ne a dakunan gwaje-gwaje na sirri, ba a wuraren da kasashen duniya ke sanya ido a kai ba, wadanda ke da’awar cewa ya rage kwanaki ta kera bam din nukiliya, me ya sa ba su goyi bayan yarjejeniar da aka cimma ba?
A wani share kuma, Zarif ya yi watsi da zargin da ake cewa Iran ta raunana a yankin.