Search
Close this search box.

Zakani : Shugaba Raeisi Ya Gyara Alkiblar Gwamnati

Alireza Zakani, daya daga cikin ‘yan takara shida a zaben shugaban kasar da za a gudanar a ranar 28 ga watan Yuni, ya ce marigayi

Alireza Zakani, daya daga cikin ‘yan takara shida a zaben shugaban kasar da za a gudanar a ranar 28 ga watan Yuni, ya ce marigayi shugaban kasar Iran Ibrahim Raeisi ya yi garambawul ga alkiblar gwamnatin kasar, yana mai jaddada bukatar samar da wata sabuwar ajandar kawo sauyi.

Zakani magajin garin Tehran kuma tsohon dan majalisa ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Laraba.

Ya kara da cewa, akwai dimbin damammaki na ci gaban kasar Iran wadanda ya kamata a yi amfani da su wajen kara karfi da ci gaban kasar.

“Dole ne mu matsa don tabbatar da su domin ganin Iran ta kasance kasa mai karfi da ci gaba.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments