Rahotanni daga Isra’ila na nuni da cewa manyan ‘yan takara a kasar na kunnen doki.
Firaministan kasar Benjamin Netanyahu da kawencen adawa da Gadi Eisenkot ke jagoranta suna kut da kut bayan zaben Isra’ila, da kujeru 51 kowanne, a cewar sabbin kuri’un sanyin safiyar Laraba.
Amma sakamakon da ko wace jam’iyya ta samu na nuna cewa Jam’iyyar Likud ta Benjamin Netanyahu ce ta sami mafi kyawun sakamako da kujeru 24, fiye da jam’iyyar Yashar ta tsohon babban hafsan sojojin kasar Gadi Eisenkot, wadda ake hasashen za ta lashe 22.
Hasashen farko kuma ya nuna cewa Jam’iyyun Larabawa na Isra’ila zai iya lashe kujeru 17 zuwa 18 a majalisar Knesset, wani abu mai cike da tarihi, wanda ake ganin sakamakon zai iya yin tasiri ga tattaunawar kafa kawance.
Tashoshin Talabijin na 11 da 13 sun nuna cewa bangarorin biyu sun yi kunnen doki, yayin da Channel 12 har yanzu ke ba wa bangaren Eisenkot dan rinjaye da kujeru 52, idan aka kwatanta da 50 ga abokin hamayyarsa.
Wasu rahotannin sun ce mai ra’ayin mazan jiya Gadi Eisenkot, wanda jam’iyarsa ta samu karamin rinjaye a kan firaMinista Benjamin Netanyahu a zaben Isra’ila, ya bayyana a daren Talata cewa yana son kafa gwamnati kuma yana adawa da gudanar da sabbon zabe.
Idan babu wani dan takara da ya sami nasarar kafa gwamnati, dole ne al’ummar Isra’ila su koma rumfunan zabe.
Kasar ta gudanar da zabe hudu tsakanin Afrilu 2019 da Maris 2021 saboda gazawar ‘yan siyasa na cimma matsaya kan yin aiki mai dorewa tare.
Wannan shi ne zaɓen ‘yan majalisa na farko tun bayan harin 7 ga Oktoba, inda yawan masu jefa kuri’a ya kai kashi 77.7%, inda mutane sama da miliyan biyar suka kada kuri’a.