Zababben Shugaban Kasar Ya Yi Alkawalin Ciki Alkawullan Yakin Neman Zabe

Zababben shugaban kasar ta Iran Ya bayyana cewa, a shirye yake ya yi wa kasa hidima da kuma al’ummar Iran, tare da yin alkawalin cika

Zababben shugaban kasar ta Iran Ya bayyana cewa, a shirye yake ya yi wa kasa hidima da kuma al’ummar Iran, tare da yin alkawalin cika dukkanin alkawuilan da ya yi a lokacin yakin neman zabe.

Zababben shugaban kasar ta Iran Ms’ud Fizishkiyan dai ya bayyana hakan ne a yayin da ya ziyarci hubbaren Imam Khumain a jiya Asabar, da a can ne ya gabatar da jawabinsa na farko bayan zabensa.

Har ila yau, Fizishkiyan ya ce zai mayar da hankali akan tattaunawa domin karfafa hadin kan kasa da kuma batutuwa da suke faruwa a duniya  ta hanayar amfani da fagagen tatalin arziki, al’adu da siyasa da al’adu.

Mas’ud Fizishkiyan ya kuma ce:

“ Ya kamata dukkaninmu mu dauki matakin tabbatar da kare manyan muradun kasa da bude wata sabuwar kafa ta kare cigaban da ake da shi.

Har ila yau, ya yi alkawalin aiki tukuru domin kawo karshen tasirin takunkuman da suke akan Iran da kuma biyawa al’umma bukatunsu.

Haka nan kuma ya yi kira ga al’ummar kasa da su ba shi dukkanin taimakon da yake bukatuwa da shi domin gina kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments