Za’ayi Sallah jana’izar Shahid Ayatollah Seyed Ali Khamenei ranar Lahadi

Masu shirya tarurukan jana’izar Jagoran juyin juya halin Mulinci na Iran mai rasuwa Ayatollah Seyed Ali Khamenei sun ce za’a yi sallar Jana’izar mirigayin a

Masu shirya tarurukan jana’izar Jagoran juyin juya halin Mulinci na Iran mai rasuwa Ayatollah Seyed Ali Khamenei sun ce za’a yi sallar Jana’izar mirigayin a gobe Lahadi da safe.

Za a yi sallah jana’izar Jagoran da danginsa hudu da suka yi shahada tare da shi a babban masallacin Tehran a sanyin safiyar Lahadi, yayin da kasar ke ci gaba da tarurukan bankwana da shi a duk fadin kasar.

Za a fara jana’izar da karfe 8:00 na safe agogon kasar, babban masallacin Khomeini da ke Tehran, inda aka ajiye gawar Jagoran a ranar Asabar don zaman makoki da tarurukan bankwana da shi.

Sauran ‘yan uwansa hudu da suka yi shahada a harin na Amurka da Isra’ila a ranar 28 ga watan Fabarairu sun hada da: Dr. Mesbah al-Hoda Bakeri Kani, surukin Jagoran; Sai seyedeh Boshra Hosseini Khamenei, ‘yarsa; da Zahra Haddad Adel, surukarsa; da Zahra Mohammadi Golpaegani, jikarsa.

Bayan sallar jana’izar a ranar Lahadi, za a gudanar da babban jerin gwanon a Tehran a ranar Litinin kafin tawagar ta yi tafiya zuwa birnin Qom a ranar Talata.

Daga nan za a ci gaba da gudanar da jana’iza da ta’aziyya a biranen Najaf da Karbala na Iraki a ranar Laraba bisa bukatar shugabannin addini da siyasa na Iraki, kafin a kammala da binne Ayatollah Seyed Ali Khamenei Haramin Imam Reza (AS) da ke Mashhad a ranar Alhamis.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted