Za’a Koma Tattaunawar Tsagaita Wuta A Gaza

A wani lokaci yau Laraba ne ake sa ran za a ci gaba da tattaunawar tsagaita wuta a Gaza da kasar Qatar ke shiga tsakani,

A wani lokaci yau Laraba ne ake sa ran za a ci gaba da tattaunawar tsagaita wuta a Gaza da kasar Qatar ke shiga tsakani, da nufin sako karin Isra’ilawan da Hamas ke garkuwa da su tun watan Oktoban bara.

Wakilan Amurka da na Isra’ila za su gana da manyan jami’an gwamnatin Qatar da kuma na Masar.

Fadar White House ta ce ana tattaunawar ne a cikin sirri da ake fatan ta kai ga cimma yarjejeniya mai inganci.

Alamu sun nuna Hamas ta rage wasu daga cikin bukatunta ga Isra’ila kafin ta amince da yarjejeniyar dindindin.

Sai dai ta ce ci gaba da kai hare-hare da sojin Isra’ila ke yi a zirin Gaza babbar barazana ce ga tattaunawar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments