A ranar Lahadi mai zuwa ne za a kada kuri’ar raba gardama akan sabon kundin tsarin mulkin kasar Guinea,wanda zai bai wa shugaban soja mai ci Mamadi Domboya damar tsayawa takara.
Kamfanin dillancin labarun Reuters ya nakalto cewa; A yau Laraba ne zai zama ranar karshe ta wayar da kai akan kada kuri’ar,wanda hakan zai zama wani mataki mai matukar muhimmanci a wannan kasa ta yammacin Afirka.
Jim kadan bayan juyin mulkin da aka yi a wannan kasa a watan Disamba na 2021, an yi dokar da majalisar Mulki ta soja ta amince da ita, wacce ta kunshi cewa; Dukkanin ‘yan majalisar Mulki ta soja ba su da hakkin tsayawa takara a fadin kasa da kuma a matakin yankuna.
Sai dai kuma a cikin sabon tsarin mulkin da za a kada kuri’ar raba gardama akansa babu wannan dokar a cikinsa.
Har ila yau, sabon kundin tsarin mulkin ya zo da sabon tsarin tsawaita wa’adin mulkin shugaban kasa daga shekaru biyar zuwa shekaru bakwai,wacce za a iya sabuntawa sau daya. Haka nan kuma a karkashin sabon tsarin mulkin za a kafa majalisar dattijai,wacce shugaban kasa ne yake da ikon nada kaso 1/3 na mamabobin wannan majalisar.
Da akwai mutane fiye da miliyan 6.7 da za su kada kuri’ar raba gardamar, za kuma a amince da shi, idan rabin wadanda su ka yi zaben su ka amince da shi.
Tun a 2024 ne dai aka tsayar da cewa za a mika wa fararen hula Mulki sai dai kuma sojojin sun saba alkawali. A watan Disamba na wannan shekarar ne aka tsayar za a yi zaben shugaban kasa.