Iran Ta Yi Nasarar Gwajin Tauraron Dan’adam Da Zai Samar Da “Internet” Ga Yankunan Karkara

Ministan sadarwa na Iran Sitar Hashimi ya bayyana cewa, an sami nasara a gwajin da aka yi na sabon tauraron dan’adam, mai suna “Nahid 2” wanda aikinsa shi ne samar da hanyoyin sadarwa na internet masu nagarta. Ministan sadarwar ya kuma ce dukkanin bangarorin tauraron dan’adam din sun yi aiki yadda ake so a yayin […]
Za A Kada Kuri’ar Raba Gardama Akan Sabon Tsarin Mulki A Kasar Guinea

A ranar Lahadi mai zuwa ne za a kada kuri’ar raba gardama akan sabon kundin tsarin mulkin kasar Guinea,wanda zai bai wa shugaban soja mai ci Mamadi Domboya damar tsayawa takara. Kamfanin dillancin labarun Reuters ya nakalto cewa; A yau Laraba ne zai zama ranar karshe ta wayar da kai akan kada kuri’ar,wanda hakan zai […]
Larijani: Iran Da Saudiyya Za Su Bunkasa Aiki Tare A Fagagen Kasuwanci Da Tsaro

Babban sakataren majalisar koli ta tsaron jamhuriyar musulunci ta Iran Dr. Ali Larijani ya bayyana cewa; Za a bunkasa aiki tare a tsakanin Iran da Saudiyya a fagagen tattalin arziki da kuma tsaro. Dr. Larijani ya bayyana hakan ne jim kadan bayan fitowar daga ganawar da ya yi da Yarima mai jiran gado na Saudiyya […]
Hukumar Tarayyar Turai Ta Gabatar Da Shawarar Jingine Aiki Da Yarjejeniyar Kasuwanci Da HKI

Hukumar tarayyar turai ta gabatar da shawara ga kasashe mambobi da su jingine aiki da yarjejeniyar da aka kulla ta kasuwanci da HKI saboda yakin Gaza. A yau Laraba ne dai hukumar tarayyar turai din ta bijiro da wannan shawarar ga kasashen mambobi,sai dai kuma babu cikakken goyon baya daga mafi yawancin kasashen kungiyar da […]
Gaza: HKI Tana Ci Gaba Da Yi Wa Falasdinawa Kisan Kiyashi A Gaza

Rahotannin da suke fitowa daga Gaza sun ce, fiye da Falasdinawa 35 ne su ka yi shahada daga Safiyar yau Laraba zuwa tsakiyar rana,sanadiyyar hare-haren da HKI take kai wa. Hakan tana faruwa ne a daidai lokacin da ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta yi gargadi akan cewa asibitocin yankin sun kusa daina aiki baki […]
Ma’aikatar Shari’ar Iran Ta Sanar Da Rataye Dan Leken Asirin Hukumar Mossad Ta Isra’ila

Ma’aikatar shari’ar kasar Iran ta sanar da zartar da hukuncin kisa kan wani ba’iraniye dan leken hukumar Mossad ta Isra”ila A safiyar yau Laraba ne ma’aikatar shari’ar kasar Iran ta sanar da zartar da hukuncin kisa kan Babak Shahbazi, dan leken asirin Mossad da aka samu da laifin hada kai da yahudawan sahayoniyya a fannin […]
Hamas Ta Zargi HKI Da Shirga Karya Don Kare Muggan Manufofinta

Kungyar Hamas ta bayyana cewa: Gmanatin mamayar Isra’ila ta ƙirƙiri ƙarya don kare kisan gillar da ta yi a Gaza Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta tabbatar da cewa: Zargin da kakakin rundunar sojin mamayar Isra’ila ya gabatar dangane da yin amfani da hasumiyai a birnin Gaza domin aikin soji ba komai ba ne illa […]
Iran Ta Bayyana Abubuwan Da Bata Amince Da Su Ba A Jawabin Bayan Taro Na Kungiyar OIC A Birnin Doha

Gwamnatin kasar Iran ta bayyana wasu abubuwan da bata amince da su ba, a jawabin bayan taro na musamman na kungiyar kasashen musulmi ta (OIC) wanda aka gudanar a birnin Doha na kasar Qatar a ranar litinin 15 gawatan Satumba da mukeciki. Sannan ta kara tabbatar da goyon bayanta ga gwagwarmayan da Falasdinawa suke yi […]
Chadi: Majalisa ta amince a baiwa shugaban kasa damar ci gaba da Mulki har karshen rayuwa

Majalisar dokokin kasar Chadi ta amince da gyare-gyaren kundin tsarin mulkin kasar da zai tsawaita wa’adin shugabancin kasar daga shekaru biyar zuwa bakwai da kuma baiwa shugaban kasar damar ci gaba da mulki na tsawon wa’adi maras iyaka. Majalisar dokokin kasar Chadi ta amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar a ranar Litinin da kuri’u […]
Iran Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Yunkurin Kasa da Ka Na Kauracewa Isra’ila

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’ilBagaei ya yi tir da samar da duk wata hulda da HKI sannan tana ganin yin haka yana dai-dai da taimaka mata ko halatta mata ayyukan ta’addancin da take aikatawa a Gaza. Kamfanin dillancin labaran Tasnem na kasar Iran ya nakalto Bagaei yana fadar haka a yau Laraba, a […]
Kwamitin bincike na MDD ya zargi Isra’ila da aikata “kisan kare dangi” a Gaza

Kwamitin bincike mai zaman kansa na Majalisar Dinkin Duniya, ya fitar da wani rahoto mai zargin Isra’ila da laifin aikata kisan kiyashi a zirin Gaza. A cikin sabon rahoto da ta gabatar a ranar Talata, MDD ta zargi shugaban kasar Isra’ila Isaac Herzog, da firaministan kasar Benjamin Netanyahu, da kuma tsohon ministan tsaro Yoav Gallant […]
Iran da Saudiyya sun bukaci hadin kan Musulmi game da halin da ake a yankin

Kasashen Iran da Saudiyya sun bukaci hadin kan hadin kan Musulmi game da halin da ake ci a yankin Wannan bayannin ya fito ne a yayin ganawar sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani da yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya Mohammed bin Salman a birnin Riyadh inda suka tattauna kan dangantakar […]
Duniya na tir da sabon farmakin Isra’ila kan Gaza

Kasashen duniya na ci gaba da yin tir da sabon farmakin soji da Isra’ila ta kaddamar kan Gaza. Kasashen Biritaniya, Faransa, Italiya, Masar, Jordan, Qatar, Spain, duk sun yi tir da farmakin kan Gaza suna masu cewa zai kara dagula halin kunci da ake ciki. Kungiyar tarayyar Turai, ta bakin Jami’ar kula da harkokin wajen […]
Akalla Falasdinawa 78 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila a Gaza

Falasdinawa 78 ne aka kashe a yau a Gaza, mafi yawansu a birnin Gaza a yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a kasa da kuma umarnin tilastawa mazauna Gaza yin kaura. An bayar da rahoton karin mutuwar mutane uku sakamakon yunwa da killace yankin. Mazauna Gaza sun bayyana tashin bama-baman a matsayin […]