Kasar Yemen ta sanar da cewa za ta ci gaba da kai hare-haren soji kan jiragen ruwan Isra’ila a wasu muhimman yankunan teku da ke gabar tekun kasar bayan cikar wa’adin da ta gindaya wa Isra’ila na ta sake bude mashigar zirin Gaza tare da bayar da damar kai agaji cikin yankunan Falasdinawa da yaki ya daidaita.
Rundunar sojin Yaman ta fitar da sanarwar a cikin daren jiya, inda ta ce za a ci gaba da kai hare-hare kan duk wasu jiragen ruwa masu alaka da ISra’ila kamar yadda Abdul-Malik al-Houthi shugaban kungiyar gwagwarmayar Ansarullah ta kasar ya bada umurni.
Tunda farko Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya bai wa gwamnatin Isra’ila kwanaki hudu ta bude hanyoyin kai kayan agaji Gaza ko ta fuskanci martini.
Sanarwar ta kara da cewa “Wannan haramcin zai ci gaba da kasancewa har sai an sake bude hanyoyin shiga Zirin Gaza kuma an ba da izinin shigar da agajin jin kai da suka hada da abinci da magunguna.
A karshe sojojin sun jaddada goyon bayansu ga al’ummar Falasdinawa masu tsayin daka a yankin zirin Gaza da kuma gabar yammacin kogin Jordan da ke mamaye da su, wadanda kuma suka fuskanci mummunar ta’addancin Isra’ila, tare da jaddada goyon bayansu ga gwagwarmayar Falasdinawa.