Yemen Tace Saudiya Ta Kai Hare Hare Har 760 Kan Kasar

Kakakin sojojin kasar Yemen ya bayyana cewa tun fara yaki na baya bayan nan jiragen yakin saudiya sun kai hare hare hae sau 760 a

Kakakin sojojin kasar Yemen ya bayyana cewa tun fara yaki na baya bayan nan jiragen yakin saudiya sun kai hare hare hae sau 760 a duk fadin kasar amma duk da haka wannan bai hana dakarun Amsarallah ci gaba da kuma samun nasara a kansu  ta ba.

Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya nakalto Burgedia Yahyah Saree yana fadar a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa, a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata kadai jiragen yakin saudia sun kai hare hare har 28 kan kasar tare da amfani da jiragen yaki samfurin F15 na kasar Amurka. Da kuma jiragen yaki samfurin Typhoon

 Wadanda suka taso daga sansanonin jiragen yaki na Taif da kuma Khamis Mushait. Kuma sun kai hare hare a kan larduna Taiz, Al-Jawf da kuma Marib na kasar Yemen.

Duk tare da wadannan hare hare sojojin Yeman sun dawo da ikon gwamnatin kasar kan yankunan kudu maso yammacin kasar wadanda suka hada da babul mandab da wau wurare masu muhimman wadanda kafin haka suna karkashin mayakan saudia ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted