Yemen Ta Kakkabo Jirgin Yakin Saudia A Kan Garin Sa’ada

Kakakin sojojin kasar Yemen Brigadier General Yahya Saree, ya bada sanarwan cewa, sojojin kasar sun sami nasarar kakkabo jirgin yakin kasar Saudia samfurin Typhoon dauke

Kakakin sojojin kasar Yemen Brigadier General Yahya Saree, ya bada sanarwan cewa, sojojin kasar sun sami nasarar kakkabo jirgin yakin kasar Saudia samfurin Typhoon dauke da makamai a kan yankin Sa’aada na kasar Yemen a ranar Laraba.

Tashar talabijan ta Presstv a nanTehran ya nakalto kakakin sojojin yana cewa, garkuwan makamai masu linzami na kasar Yemen ya sami jirgin yakin na saudia a tsakiyarsa ya kuma kakkaboshi kasa a kan yankin. Ya kumakara da cewa jirgin ya taso ne daga sansanin sojojin sama na kasar saudia da ke Taif, dauke da makamai masu linzami dauke da makamai masu linzami samfurin surface ta Air.

 A cikin watan da ya gabata ma , sojojin yemen masu kula da sararin samaniyar kasar ta Yemen sun kakkabo wani jirgin yakin saudiya samfurin F-15 kirar kasar Amurka a kan yankin Marib na kudancin kasar.

Banda haka sojojin kasar Yemen sun sha kakkabo jiragen yakin kasar da saudia marasa matuka sau da dama a kan kasar. Inda a ranar talatar da ta gabata ma, sojojin sun kakkabo jirgin saman yaki samfurin Loong II kirar kasar China a kan lardin Sa’adda na kasar ta Yemen.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted