Yemen Ta kai Hari Da Makami Mai Linzami Kan Isra’ila

Dakarun kasar Yemen sun sanar da kai farmaki kan birnin Tel Aviv da makami mai linzami kirar “Palestine-2”, lamarin da ke nuni da karuwar tashe-tashen

Dakarun kasar Yemen sun sanar da kai farmaki kan birnin Tel Aviv da makami mai linzami kirar “Palestine-2”, lamarin da ke nuni da karuwar tashe-tashen hankula a yankin a daidai lokacin da ake ci gaba da rikici a Gaza.

A cikin wata sanarwa da kafar yada labaran Yaman ta Al-Masirah ta fitar, Birgediya Janar Yahya Saree kakakin rundunar sojin Yaman ya dauki alhakin kai harin.

A cewar Saree, an yi nasarar kai harin kan wani yankin”Jaffa da aka mamaye”,.

“Mun kai hari a wani wurin soji mallakar makiya Isra’ila a Jaffa da suka mamaye ta hanyar amfani da makami mai linzami samfarin Palestine-2,” in ji Saree. ” Cikin ikon Allah aikin ya cimma manufarsa.”

Saree ya jaddada cewa, ya bayyana hakan a matsayin martani ga laifukan da gwamnatin Isra’ila ke ci gaba da yi kan Falasdinawa a Gaza.

“Wannan farmakin wani bangare ne na aikin mu na tsayawa tare da al’ummar Falastinu da ake zalunta,” inji shi.

kuma dukkan ‘yan Yemen mun shirya tsaf domin tunkarar zaluncin Isra’ila, da Amurka da kuma Birtaniya.”

Kakakin rundunar sojin Yaman ya kuma lashi takobin ci gaba da aiyukan soji domin nuna goyon baya ga gwagwarmayar Gaza muddun Isra’ila ta ci gaba da kai hare-haren.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments