Rundunar sojin Yemen ta ce ta kai hare-haren soji guda bakwai ta amfani da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka a cikin Saudiyya, ciki har da filin jirgin saman Sarki Khalid na Riyadh, cibiyoyin Aramco da ke Yanbu, da kuma matatar mai ta Rabigh.
A cikin wata sanarwa kakakin rundunar sojin Yeman Birgediya Janar Yahya Saree ya ce an kai hare-haren ne “don mayar da martani ga mummunan harin da Saudiyya ta kai wa Yemen”.
Janar Saree ya ce Saudiyya ta kai hare-hare sama da 100 a cikin awanni 24 da suka gabata kan kayayyakin more rayuwa na fararen hula a babban birnin kasar, Sana’a, da sauran larduna, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da kuma jikkata wasu.
Sanarwar ta ce jimillar hare-haren sama da makamai masu linzami da aka kai wa Yemen tun farkon wannan tashin hankali sun kai 3,123.
A cewar sanarwar, harin farko an kai shi kan filin jirgin saman King Khalid na Riyadh a matakai biyu.
Na biyu an kai shi kan Aramco da ke Yanbu, na uku kuma kan matatar mai ta Rabigh.
Tunda farko Rahotanni sun ce Saudiyya ta kai hare-haren ta sama da makamai masu linzami a yankuna daban-daban na kasar Yemen; inda daya daga cikin hare-haren ya shafi masaukin ma’aikata a wani kamfanin siminti, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane takwas tare da jikkata wasu fiye da goma.
Gidan talabijin na Al-Masirah mai watsa shirye-shirye da harshen Larabci a Yemen ya bayar da rahoton cewa, jiragen yakin Saudiyya sun kai hare-haren ta sama kusan 20 a yankin Mokha da ke lardin Ta’iz.