Yemen Ta Kaddamar Da Hari Kan Garin Jaffa Na Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Sojojin Yemen sun kai hari kan garin Jaffa na haramtacciyar kasar Isra’ila da makami mai linzami Sojojin kasar Yemen sun sanar da cewa: Sun kai

Sojojin Yemen sun kai hari kan garin Jaffa na haramtacciyar kasar Isra’ila da makami mai linzami

Sojojin kasar Yemen sun sanar da cewa: Sun kai hari da makami mai linzami kan yankin Jaffa da yahudawan sahayoniyya  suka mamaye a yau Laraba.

A sanarwar da rundunar Sojin Yemen ta fitar ta bayyana cewa: Sojojinta sun kaddamar da hari da makami mai linzami kirar “Falasdinu 2” kan yankin Jaffa dake karkashin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila, kuma sanarwar ta tabbatar da cewa: Wannan farmakin ya cimma manufar da ake so cikin nasara, sannan sojojin Yemen suna ci gaba da gudanar da ayyukan soji a kan gwamnatin makiya ta yahudawan sahayoniyya ‘yar mamaya, kuma wadannan hare-haren ba za su tsaya ba, matukar ba a dakatar da kai farmakin da ake kai wa Gaza ba, tare da kawo killace yankin saboda da matakan zalunci.

Majiyar rundunar sojin ta Yemen ta kuma jaddada cewa: Hare-haren da take kai wa na daukan fansa ne kan zaluncin da yahudawan sahayoniyya suke gudanarwa kan al’ummar Falastinu da ‘yan gwagwarmayarsu, kuma mayar da martani ne kan kisan kiyashin da ake yi wa ‘yan uwansu Falasdinawa a Gaza, kuma mataki ne na biyar na goyon bayan jihadi mai tsarki da ke mayar da martani ga zaluncin da haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai wa kan kasar Yemen.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments