Yemen: Jiragen Yakin Amurka Da Ingila Sun Kai Wa Yemen Hare-hare

Gwamnatin Yemen ta sanar da cewa, jiragen yakin Amurka da Birtaniya sun kai hare hare a cikin biranen San’aa da kuma Sa’adah, har sau 15

Gwamnatin Yemen ta sanar da cewa, jiragen yakin Amurka da Birtaniya sun kai hare hare a cikin biranen San’aa da kuma Sa’adah, har sau 15 a daren jiya.

Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta ambaci cewa; Daga cikin yankunan da aka kai wa harin da akwai “Telfiziyun’, al-Hafa’ da Jirban da suke a kudancin birnin Sanaa.

Wani jami’in gwamnatin  San’aa Ali al-Qahhum ya bayyana cewa; Manufar harin  shi ne hana Yemen cigaba da taimakawa Falasdinawa da Lebanon,sai dai hakan ba zai faru ba.

Ali al-Qahhum ya fadawa Amruka da Birtaniya cewa, karfinmu yana karuwa, kuma tabbas za mu mayar da martani.”

Ministan tsaron Amurka ta bayyana cewa; Manyan jiragen yakin Amurka B2 ne aka yi amfani da su wajen kai hari.

Wasu  yankunan da aka kai wa harin, bayan San’aa da Sa’adah, su ne al-lahyah,dake yammacin Hudaidah.

Kwanaki biyu da su ka gabata ne dai sojojin Yemen su kai hari akan jiragen ruwan Amurka da su ka hada da Olympic Sprit na Amurka, da kuma St John.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments