Yemen: Janar Yahya Sari Ya Sanar Da Kai Wa Manyan Jiragen Ruwan Amurka Hari

Kakakin sojan kasar Yemen Janar Yahya Sari ya sanar a yau Juma’a cewa, a cikin sa’o’i 48 da su ka wuce, sojojin na Yemen sun

Kakakin sojan kasar Yemen Janar Yahya Sari ya sanar a yau Juma’a cewa, a cikin sa’o’i 48 da su ka wuce, sojojin na Yemen sun aiwatar da hare-hare masu yawa akan manyan jiragen ruwan Amurka masu dakon jiragen yaki, da kuma akan manufofin HKI a Yafa.

Jirgin dakon jiragen yakin da sojojin Yemen din su ka kai wa hari, shi ne na “USS Harry Truman” da kuma wasu kananan jiragen ruwan yaki da suke tare da shi a arewacin tekun “Red-Sea”.

Bugu da kari kakakin na sojojin Yemen ya sanar da cewa sun kai wasu jerin hare-haren a jiya Alhamis akan wasu manufofin na HKI dake Yafa,  ( Tel Aviv) ta hanyar harba jiragen sama marasa matuki guda uku, kuma duk sun isa inda aka tura su.

 A gefe daya dubun dubatar mutanen Yemen din sun yi gangami a yau Juma’a a biranen Ma’arib,sa’adah, raimah da Ta’iz da Hijjah. An  yi gangamin ne dai a cikin wuraren 35 a fadin kasar ta Yemen.

A karshen gangamin an fitar da bayani wanda ya kunshi jaddada cigaba da goyon bayan al’ummar Falasdinu da kuma yin Allawadai da keta hurumin wuraren masu tsarki na musulunci da ‘yan sahayoniya suke yi.

Mutanen Yemen dai sun sha nanata cewa za su cigaba da hana jiragen ruwa wucewa zuwa HKI, haka nan kuma kai wa manufofin ‘yan sahayoniyar hare-hare har zuwa lokacin da za a dakatar da kai wa Gaza hari da kuma dauke  wa yankin takunkumi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments