Gwamnatin kasar Yemen wacce kungiyar Ansarallah take jagoranta ta bayyana cewa ziyarar da ministan harkokin wajen HKI ya kai yankin Somalilanda na kasar Somalia ba tare da izinin bay a halattawa kasar kai mata hare-hare a kan abinda take da shi a yankin.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin waje na riko Abdullah Wahid Abu Ras yana fadar haka ya kuma kara da cewa ziyarar da Gidion Sa’ar ya kai yankin Somaliland wani babban kuskure ne wanda ya sabawa dokokin kasa da kasa. Banda haka ya sanya HKI kasa wacce take take dokokin kasa da kasa tare da keta hurumin kasashen yanking abas ta Tsakiya.
Ras ya yi kira ga kasashen yankin da kuma kasashen Musulmi su ki amincewa da wannan keta hurumin da HKI take yi a yankin. Saboda samuwarta a Somalilanda barazane ce ga tsaron tekun Red Sea da kuma tekun Umman. Har’ila yau zata zama barazana ga dukkan kasashen larabawa da musulmi a yankin.
Kwanaki 10 da shelenta amincewa da Somaliland HKI ta tura ministan harkokin wajenta zuwa yankin. Somaliland dai ta shelanta ballewa daga kasar Somalia ashekara 1991 amma ba kasa ko guda da ta amince da samuwarta.