Yemen: An Kashe Sojojin Saudia Da Dama  A Kudu

Sojojin kasar Yemen sun bayyana cewa sun sami nasarar kashewa da kuma raunta taron sojojin masu goyon bayan gwamnatin kasar Saudia a karo na biyu

Sojojin kasar Yemen sun bayyana cewa sun sami nasarar kashewa da kuma raunta taron sojojin masu goyon bayan gwamnatin kasar Saudia a karo na biyu a lokacinda suke kokarin kaiwa da mashigar ruwa ta babul Mandab a karo na biyu.

Tashar talabijan ta Al-mayadeen ta kasar Leban ta nakalto majiyar sojojin Yemen na cewa sun lalata tankunan yaki 22 sun kuma kashe wasu dadama a fafatwar ranar Alhamis.

Labarin ya kara da cewa, hakan ya faru ne a lardin Lahhaj, y ace sun kai masu hare hare da adadi mai yawa na makamai masu linzami samfurin bilistic da kuma wasu makamai masu nauyi.

Labarin ya kara da cewa sun sami labarin isar mutocin daukar marasa lafiya fiye da 30 zuwa birnin Aden dau–ke da gawakinsu da kuma wadanda aka jiwa rauni daga sojojin saudia.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted