Rahotanni daga Isra’ila na cewa an jiyo karar jiniya ta gargadi a sassa daban daban na kasar sakamakon wani harin makamai mai linzami da ya doshi kasar daga Yeman.
Rundinar sojin Isra’ila ta ce ta kakkabo wani makami mai linzami da aka harbo daga kasar Yeman.
Kafofin yada labaran Isra’ila sun ruwaito samun barna a unguwar Ramat Aviv da ke arewa maso yammacin Tel Aviv.
Kakakin Rundunar Sojin Yeman Birgediya Janar Yahya Saree ya ce zai gabatar da “mahimman bayani” a cikin sa’o’i masu zuwa.
Tashar talabijin ta al-Masirah ta kasar Yemen ta ce kaddamar da harin na ranar Alhamis martani ne ga wasu hare-haren wuce gona da iri na Isra’ila kan babban birnin kasar Sana’a, da suka hada da na’urorin samar da wutar lantarki guda biyu a birnin, da kuma wasu hare-hare da suka kai 6 kan birnin al-Hudaidah da ke yammacin kasar Yemen da bututun mai na Marib–Ras Isa, babban bututun mai na kasar Yemen da ke kudu maso yammacin kasar.
To saidai Sojojin Isra’ila sun sanar da cewa, sun kai hari kan ‘yan Houthi a kasar Yemen, bayan harin na makami mai linzami.
Yeman dai na kai hare-hare kan Isra’ila ne domin nuna goyan baya ga al’ummar falasdinu.