Yemen ta tabbatar da sake harba wabi makami mai linzami mai gudun tsiya kan Isra’ila.
Da yake sanar da hakan Birgediya Janar Yahya Saree, kakakin rundunar sojin kasar, ya sanar a wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin yau Lahadi cewa, bangaren dakarunsu na makamai masu linzami sun harba makami mai linzami samfarin Falasdinu-2 a tashar wutar lantarki ta Orot Rabin da ke Hadera, a yankin gabar tekun Mediterranean da Isra’ila ta mamaye.
Matakin ya cimma burin da ake so cikin nasara,” in ji Saree.
Ya kuma jaddada kudirin kasar Yemen na tallafawa Falasdinawa a Gaza, yana mai bayyana wannan aiki a matsayin wani bangare na “addini, da’a, da kuma hakkin bil adama na Yemen.”
Saree ya ci gaba da cewa matakin soji zai ci gaba da kasancewa muddin ana ci gaba da kai hare-hare kan Gaza.