Yawan Yan Jarida Da HKI Ta Kashe A Gaza Sun Kai 239

Majiyar gwamnatin Hamas a Gaza ta bada sanarwan cewa sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila(HKI) sun kashe wani dan jirida a Gaza, wanda ya kawo adadinn yan

Majiyar gwamnatin Hamas a Gaza ta bada sanarwan cewa sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila(HKI) sun kashe wani dan jirida a Gaza, wanda ya kawo adadinn yan jaridan da ta kashe tun farkon watan octoban shekara 2023 zuwa 239.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar kiwon lafiya a gaza na cewa a jiya litinin sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa a unguwar Sabra na birnin Gaza, daya daga cikinsu dan jarida ce wanda ake kiransa Islam al-Koumi.

Majiyar ta kara da cewa an kashe Koumi cikin makonin da suka gabata, amma ba’a gano gawarta ba sai jiya litinin.

Sannan wata Marwa Musallam an binneta karkashin burbushin gine gine, duk kukanta na neman taimaka ba wanda ya ji kararta har ta rasu. Kafin haka akwai wadanda suka ji kararta amma sojojin mamayar sun ki barin masu ceto su isa wadanda wanda ya kai ga shahadarta. Labarin ya bayyana cewa ba’a sami damar fitar da gawarta ba sai bayan kwanaki 45.

 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted