Yawan mutanen Da Suka Mutu A Kissan Afirka Da Kudu A Ranar Lahadi  Ya Kai 10

Yawan mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar kisa kan mai uwa da wabi wanda wasu yan bindiga suka yi a wani wuri kusa da birnin

Yawan mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar kisa kan mai uwa da wabi wanda wasu yan bindiga suka yi a wani wuri kusa da birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu a ranar lahadin da ta gabata ya kai 10, inji majayar yansandan kasar.

Shafin yanar gizo na labarai Afrika News ya nakalto majiyar yansandan kasar Afrika ta kudu na cewa, sun gano mutane biyu daga cikin yan bindigan da suka aiwatar da kissan ranar Lahadin da ta gabata, a garin Bekkeredal mai tazaran kilomita 46 daga yammacin birnin Johannesburg, inda mutane 10 suka rasa rayukansu, wannan wasu 9 suna jinya a asbitoci.

Labarin ya kara da cewa mutane 12 dauke da bindigogi sun fara barin wuta kan mutane da misalign karfe daya na dare, sunci gaba da kashewa kan mai uwa da wabi a cikin motoci biyu, suna tserewa daga wurin.

Maj. Gen. Fred Kekana, kwamishinan yansanda a yankin Gauteng, ya ce sun gano mutane 2 daga cikin yan bindigan duk da cewa basu shiga hannu ba. Yace an kama wanda yake da shagon shan barasa inda abin ya faru tare da tuhumarsa da saida barasa a wurin ba tare da amincewar gwamnati ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted