Search
Close this search box.

Yawan Falasdinawa Da Suka Yi Shahada Sun Kai 37,925 A Yakin Da Ake Yi A Gaza

Yawan Falasdinawa da suka yi shahada a Gaza sakamakon hare-haren wuce gona da irin gwamnatin h.k.Isra’ila sun kai mutane 37,925 Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta

Yawan Falasdinawa da suka yi shahada a Gaza sakamakon hare-haren wuce gona da irin gwamnatin h.k.Isra’ila sun kai mutane 37,925

Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta sanar a jiya Talata cewa: Adadin Falasdinawa da suka yi shahada a yankin Gaza ya karu zuwa 37,925, wadanda akasarinsu yara ne da mata, tun bayan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta fara kai hare-haren wuce gona da iri kan al’ummar Falasdinu a ranar 7 ga watan Oktoban bara.

Ma’aikatar ta kara da cewa: Adadin wadanda suka jikkata ya karu zuwa 87,141 tun daga farkon harin. Sannan ta yi nuni da cewa gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ta aiwatar da kisan kiyashi har sau 3 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, inda suka yi sanadiyyar shahadan Falasdinawa 25 tare da jikkatan wasu 81 na daban.

Kamar yadda ta jaddada cewa: Har yanzu akwai wani adadin Falasdinawa da suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da irin yahudawan sahayoniyya da suka kasance a karkashin baraguzan gine-gine da kuma kan tituna, kuma motocin daukar marasa lafiya da jami’an tsaron farin kaya sun kasa kai musu dauki saboda killace yankin da aka yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments