Yawan Falasdinawa Da Suka Yi Shahada A Gaza Sun Kai 72,608

Adadin mutanen da suka yi shahada sakamakon hare-haren da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan Gaza ya kai 72,608 Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu a

Adadin mutanen da suka yi shahada sakamakon hare-haren da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan Gaza ya kai 72,608

Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu a yankin Gaza ta ruwaito cewa: Adadin mutanen da suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da irin da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suke kai wa kan yankin Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, ya karu zuwa shahidai 72,608, baya ga wadanda suka jikkata da yawansu ya kai 172,445.

A cikin rahoton kididdiga da ta fitar a ranar Asabar, Ma’aikatar ta bayyana cewa: Asibitoci sun karbi shahidai bakwai a cikin awanni 48 da suka gabata, ciki har da sabbin wadanda suka yi shahada guda hudu da kuma uku da aka gano a karkashin baraguzan gine-gine, da kuma mutane 26 da suka jikkata.

Ma’aikatar ta tabbatar da cewa: Jimillar wadanda suka mutu tun bayan tsagaita wuta a ranar 11 ga Oktoba ya kai 828, yayin da adadin wadanda suka jikkata ya kai 2,342, baya ga zakulo shahidai 767 daga karkashin baraguzan gine-gine.

Ta lura cewa da yawa daga cikin wadanda abin ya shafa suna karkashin baraguzan gine-gine da kuma kan tituna, yayin da motocin daukar marasa lafiya da na kare farar hula har yanzu ba su iya isa gare su ba saboda yanayin tsaro da matsalolin kayan aiki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted