Yar rahoton tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta ji rauni a jiya Talata a lokacinda take bada rahoto kai tsaye daga wani sansanin yan gudun hijira a yankin yamma da kogin Jordan.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa Naqqa Hamed tana bada rahoton hare-hare na baya-bayan nan wanda sojojin HKI suka kai kan sansanin yan gudun hijira falasdinawa da ke Qalandia kusa da birnin Qudus a jiya Talata, a lokacinda wani sojan HKI ya harbe ta da albarusin ruba a kafa. Labarin ya kara da cewa, bayan an kaita asbiti likitoci sun bayyana cewa ta ji rauni amma ba mai hatsari bane.
Sojojin HKI dai suna gadin sansanin yan gudun hijirar ta ko ina, kuma a jiyan kadai sun kama wasu matasa falasdinawa a sansanin sun yi gaba da su. Banda haka motocin Bulldozers wadanda suke samun rakiyar sojojin mamayar sun rusa shaguna da wararen kasuwanci na falasdinawa kusa da sansanin yan gudun hijira na Qalaqelian.
A halin yanzu dai gwamnatin yahudawa tana wasu gine gine a yankin inda take nufin raba birnin Qudus da garin Ramallah kwata-kwata, inda Falasdinawa da dam,a suke zama.