Yan Wasan Kwallon Futsal Na Iran Sun Zama Zakara A Asia

Kungiyar kwallon kafa ta ‘Futsal’ ta kasar Iran ta zama zakara, kuma ta dauki kofin gasar Futsal ta kasashen Asia a wasa ta karshe wacce

Kungiyar kwallon kafa ta ‘Futsal’ ta kasar Iran ta zama zakara, kuma ta dauki kofin gasar Futsal ta kasashen Asia a wasa ta karshe wacce aka gudanar a birnin Jakarta na kasar Indonasia a jiya Asabar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kungiyar karkashin mai hurar da su Hossein Tayebi  sunsake lashe gasar ta shekara ta 2026 wanda ya kara daga matsayin kasar a fagen wasan Futsala a Asia da kuma duniya.

Labarin ya kara da cewa an gudanar da gasa ta karshe ne a filin wasan Arena da ke Jakarta tare da yan kallo kimani 16,500. Kuma yan wasan kasashen biyu sun yi wasa sosai sai dai daga karshe sun kai ga bugun fenalto wao daga kai sai gola inda kasar Iran ta sami nasara a kan kasar Indonisia mai masaukin bakin gasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted