‘Yan tawayen Kungiyar M23 Sun Kwace IKo Da Wani Sabon Gari A Kasar DRC

Kungiyar ‘yan tawayen ta kwace iko da garin Minova a gabashin kasar DRC wanda yake da muhimmanci akan hanyar zuwa birnin Goma. Mahukuntan kasar ta

Kungiyar ‘yan tawayen ta kwace iko da garin Minova a gabashin kasar DRC wanda yake da muhimmanci akan hanyar zuwa birnin Goma.

Mahukuntan kasar ta DRC sun sanar da faruwar hakan a jiya Talata, da hakan ya haddasa ficewar dubban mutane daga yankin zuwa inda suke zaton samun aminci.

A cikin makwannin baya- bayan nan dai kungiyar ‘ya tawayen ta ka me iko da muhimman garuruwa masu muhimmanci a cikin wannan yankin na gabashin kasar DRC.

Gwamnan gundumar Kivu ta kudu, Jean Jacques Purusi ya tabbatar da kama garin na Minova, sannan ya kara da cewa, ‘yan tawayen sun kuma kama garuruwan da ake hako ma’adanai na Limbishi, Numbi da kuma Shanje. Haka nan kuma sun kama garin Bweremana dake a gundunar Kivu ta Arewa.  Sojojin kasar ta DRC sun tabbatar da cewa, ‘yan tawayen sun iya kutse a cikin garuruwan Minova da Bwereman.

Kungiyar M23 daya ce daga cikin kungiyoyin da suke dauke da makamai kusan su 100 a cikin kasar ta DRC da suke kokarin shimfida ikonsu a yankuna da suke da ma’adinai.

Yaakin da ake yi a wannan kasa ya dade, kuma ya mayar da mutane miliyan 7 zama ‘yan gudun hijira.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments