Search
Close this search box.

Yan Ta’adda Sun Kashe Mutane 39 A Kudu Maso Yammacin Kasar Pakistan

Yan ta’adda sun kashe mutane akalla 39 a yankin kudu maso yammacin kasar Pakisatan, inda mayakan kungiyar ‘yentar da kabilar baloch’ ko ‘Baloch Liberation Army’

Yan ta’adda sun kashe mutane akalla 39 a yankin kudu maso yammacin kasar Pakisatan, inda mayakan kungiyar ‘yentar da kabilar baloch’ ko ‘Baloch Liberation Army’ (BLA) na kasar Pakistan ta dauki alhakin aiwatar da ayyukan ta’addancin a yau Litinin.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasarn Faransa ya nakalto Shahid Rind kakakin lardin Balochistan yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa a labarin da suka samu yan bindiga fiye da dozun guda ne suka kashe akalla mutane 23 daga cikinsu, a kan wani babban titi wanda ya hada lardin Balochestan da kuma lardin Punjab. Yace yan ta’addan sun tsaida mutoci da dama sannan suka bisu daya bayan daya suna fitar da yan lardin Punjab suna kashewa.

Labarin ya kara da cewa yan ta’addan sun kashe wasu mutane 10 a lardin Kalat,  wanda ya hada da wasu sojojin sa kai 4 da kuma dansanda guda. Rind ya kammala da cewa sauran kashe-kashen sun auku ne a lokacinda yan ta’addan suka tada nakiya a kan wata gadar layin doko a gundumar Bolan na yankin.

Firai ministan kasar Pakisatan Shehbaz Sharif ya bayyana kaduwarsa da ayyukan ta’adanci a kudancin kasar, kuma ya yi alkawarin daukar matakan da suka dace.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments