Hukumar kula da ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa sama da mutane miliyan daya ne akasari mata da kananan yara ne suka rasa matsugunansu a Syria tun bayan da ‘yan tawaye suka kaddamar da farmaki a ranar 27 ga watan Nuwamba wanda ya kai ga kifar da gwamnatin Bashar Al-Assad a ranar Lahadi.
“Ya zuwa ranar 12 ga watan Disamba, mutane miliyan 1.1 ne suka rasa matsugunansu a fadin kasar tun bayan barkewar tashe-tashen hankula a ranar 27 ga watan Nuwamba.
“Mafi yawansu mata da yara ne,” in ji ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya OCHA a cikin wata sanarwa.
Kasar Siriya dai ta shiga rashin tabbas bayan da gungun ‘yan adawan dake dauke da makamai suka sanar da kifar da mulkin tsohon shugaban kasar Bashar Al-Assad.