A daidai lokacin da yahudawa suke bikin shiga sabuwar shekara, wasu ‘yan sahayoniya sun yi kutse a cikin masallacin Kudus, inda su ka rika yin busa da kuma rawa a cikin masallacin na Kudus.
Wannan dai ba shi ne farkon lokacin da ‘yan share wuri zauna suke yin kutse a cikin masallacin kudus ba domin tsokanar musulmi.
Daga fara yakin Gaza zuwa yanzu, ‘yan share wuri zauna din sun rika kutsawa a cikin masallacin na Kudus, a karkashin rakiya ‘yan sandan HKI da kuma wasu ‘yan siyasa.
Watanni kadan da su ka gabata, wasu ‘yan siyasar HKI sun rika yin kira da a rushe masallacin na Kudus domin a gina dakin bautar yahudawa a bagirensa.