Rahotanni sun bayyana cewa yan sandan kasar faransa sun yi amfani da hayaki mai sa yawaye da ruwan zafi wajen tarwatsa masu zang zangar neman gwamanti da shugaban kasar Emanuel marcron da minsitan ilimi na kasar su yi murabus daga mukamansu,
A yau ne aka yi taho mu gama tsakanin jami’an yan sanda da masu zanga-zangar inda aka jikkata da dama daga cikinsu tare da kuma kama wani adadi mai yawa a yayin taho mu gama. inda masu zanga zangar suke ta fitowa adaidai lokacin da yan sanda ke amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa su,
Rahotanni sun bayyana cewa mutane da dama ne suka harci zanga-zangar a yau domin nuna goyon bayansu ga dalibai dake zanga-zanga a kasar, sabuwar zanga-zanga ta zo ne adaidai lokacin da ake samun rashin jituwa tsakanin gwamnati da kuma daliban, inda wasu daga cikin su ke ganin matakin da suka dauka a ranar talata zai zama mafarin samun gagarumin sauyi a zanga-zangar da suke yi