‘Yan Sahayoniyya Suna Ci Gaba Da Gudu Daga Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Jaridar haramtacciyar kasar Isra’ila ta watsa rahoton cewa: Yahudawan sahayoniyya 82,700 ne suka tsere daga Isra’ila cikin shekara ta 2024 Jaridar Yedioth Ahronoth ta haramtacciyar

Jaridar haramtacciyar kasar Isra’ila ta watsa rahoton cewa: Yahudawan sahayoniyya 82,700 ne suka tsere daga Isra’ila cikin shekara ta 2024

Jaridar Yedioth Ahronoth ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta sanar da cewa: Adadin yahudawan sahayoniyya da suka tsere daga haramtacciyar kasar ta Isra’ila zuwa wasu kasashen duniya a cikin shekarar da ta gabata ta 2024 ya kai kusan mutane 82,700.

A farkon wannan sabuwar shekara ta 2025, Cibiyar Kididdiga ta Tsakiyar Isra’ila ta bayyana cewa: Adadin da ba a saba gani ba a tarihin haramtacciyar kasar Isra’ila na yahudawan sahayoniyya sun fice daga cikin haramtacciyar kasar Isra’ila a cikin shekara ta 2024, domin gujewa yakin da ake ci gaba da yi.

Rahoton da hukumar kididdiga ta tsakiya ta fitar ya kuma yi karin haske kan ma’auni na kaura daga haramtacciyar kasar Isra’ila zuwa wasu kasashen duniya, wanda ke auna bambancin yawan yahudawan da suka koma haramtacciyar kasar Isra’ila da kuma wadanda suka bar ta.

A cewar jaridar, a karshen shekarar 2024, ma’aunin shige-da-fice mutane a haramtacciyar kasar Isra’ila ya canza sosai, wanda ke nuni da cewa: An yi mummunan hasara mai yawa na yawan jama’a a Isra’ila, sakamakon ƙauran yahudawan sahayoniyya daga haramtacciyar kasar zuwa ƙasashen waje domin rayuwa cikin aminci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments