‘Yan Sahayoniyya Sun Kai Hare-Haren Wuce Gona Da Iri Kan Kasar Lebanon

Wasu munanan hare-hare da haramtaciyar kasar Isra’ila ta kai kan kasar Lebanon ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane tare da jikkatan wasu na daban Rahotonni

Wasu munanan hare-hare da haramtaciyar kasar Isra’ila ta kai kan kasar Lebanon ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane tare da jikkatan wasu na daban

Rahotonni sun bayyana cewa: Mutane fiye da 356 ne ‘yan kasar Lebanon suka yi shahada, yayin da wasu 1,246 suka samu raunuka, sakamakon munanan hare-haren ta’addanci sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan garuruwa da kauyuka da suke kudancin kasar Lebanon.

Ministan lafiya na kasar Lebanon ya bayyana cewa: Sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hare-haren ne kan wurare da dama ciki har da kan asibitoci, cibiyoyin kiwon lafiya da motocin daukar marasa lafiya.

Yana mai fayyace cewa: Alkaluman yawan mutanen da suka rasa                                     rayukansu sakamakon wannan ta’asar ba a taba ganin irinsa ba, domin kimanin mutane 5,000 ne suka samu raunuka tun farkon fara wannan ta’asar, ciki har da harin dabbanci na Bejrat, da kuma na yankin Kudancin kasar.

Ministan na Lebanon ya kara da cewa: Alkaluman da hare-haren wuce gona da iri suka ritsa da su sakamakon wannan ta’asar ba a taba ganin irinsa ba, yana mai cewa: Mafi yawan kasashe ‘yan uwa da abokan arziki da dama sun bayyana aniyarsu ta ba da taimako.

Ministan lafiya na kasar Lebanon ya tabbatar da cewa: Dukkan wadanda abin ya shafa fararen hula ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments