‘Yan Majalisar Faransa Sun Tsige Firaministan Kasar Michel Banier

‘Yan Majalisa a Faransa sun kada kuri’ar yanke-kauna, wadda ta yi sanadiyar tsige firaministan kasar Michel Banier kwanaki 91 kacal da rike mukamin. Jam’iyyun hamayya

‘Yan Majalisa a Faransa sun kada kuri’ar yanke-kauna, wadda ta yi sanadiyar tsige firaministan kasar Michel Banier kwanaki 91 kacal da rike mukamin.

Jam’iyyun hamayya ne suka yi kira da aka kada ƙuri’ar bayan da Mr Banier ya yi amfani da karfin ikonsa wajen tilasta garambawul a harkokin tsaro.

Mafiya rinjayen yan majalisar sun kada kuri’ar amincewa da tsige shi da kuri’a 331, kimanin wata uku bayan Shugaban kasa Emmanuel Macron ya nada shi.

Barnier dai zai ci gaba da rike mukamin kafin shugaban kasar ya nada wanda zai maye gurbinsa.

Kuri’ar da aka gudanar jiya Laraba, ta kasance irinta ta farko tun shekara ta 1962.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments