Rahotanni sun bayyana cewa Yan majalisar dokokin kasar Aljeriya za su kada kuri’a amince da harmatar mulkin mallakar kasar faransa a Aljeriya, matakin da kakakin majalisar ya bayyana shi a matsayin wani ginshiki a tarihin kasar.
Ana sa rana yan majalisar za su tattauna kan batun dokar a ranar laraba mai zuwa adaidai lokacin da rikicin diplomasiya tsakanin Aljeriya da Paris ke kara kamari,
Faransa tayi mulki kasar Aljeriya sama da shekaru 130 kuma an zargeta da aikata laifuffuka kan alummar kasar da suka hada da kisan kare dangi Azabtarwa, lalata tattalin arziki, da kum nuna wariya ga musulmi yan asalin kasar .
Kasar Aljeriya ta samu yancin kai ne a shekara ta 1962 bayan da aka gwabza kazamin yaki da yayi sanadiyar mutuwar mutane miliyan 1.5, dubbbai kuma suka jikkata yayin da wasu adadin mai yawa kuma ya yi batan dabo. A shekara ta 2018 kasar faransa ta bayyana alhakin gallazawa jama’a.