Ya zuwa yanzu adadin ‘yan jaridan da “Isra’ila” ta kashe a Gaza ya kai 240 tun farkon yakin kisan kare dangi a zirin Gaza, bayan kashe dan jarida mai daukar hoto Khaled Muhammad al-Madhoun, wanda ke aiki da gidan talabijin na Falasdinu, a cewar wata sanarwa da ofishin yada labarai na gwamnatin Falastinu ya fitar.
Ofishin ya yi Allah wadai da kisan gilla da sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suke ke yi wa ‘yan jarida, tare da yin kira ga kungiyar ‘yan jarida ta kasa da kasa, da kungiyar ‘yan jarida ta Larabawa, da dukkanin kungiyoyin ‘yan jarida na duniya da su yi Allah-wadai da wadannan laifuffuka.
A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Asabar, ofishin ya dora alhakin hakan a kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila, da gwamnatin Amurka, da kuma kasashen da ke da hannu wajen taimaka domin aiwatar da kisan kare dangi, irin su Birtaniya, Jamus, da Faransa, wadanda ke da alhakin wadannan munanan laifuka a kan wuyayensu.
Ofishin yada labaran gwamnatin Gaza ya yi kira ga al’ummomin kasa da kasa, da kungiyoyin kasa da kasa, da dukkanin bangarori masu alaka da aikin jarida da kafofin watsa labaru na duniya, da su yi Allah wadai da laifukan Haramtacciyar Kasar Isra’ila, da kokarin dakatar da ita, da ci gaba da yunkurin gurfanar da ita a gaban kotunan kasa da kasa, tare da kuma gurfanar da sojojin da suka aikata kisan kiyashi.