A Ivory Coastana ci gaba da kirga kuri’u bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar a jiya Asabar.
An kira sama da masu jefa kuri’a miliyan 8 zuwa rumfunan zabe a rumfunan zabe sama da 25,000 a fadin kasar.
A kasar da ta fuskanci mummunan yakin basasa, zaman lafiya yana daya daga cikin manyan abubuwan da jama’a ke fata.
‘Yan takara biyar ne suka fafata a wannan zaben, ciki har da Alassane Ouattara, mai shekara 83 wanda ke neman wa’adi na hudu.
Duk da cewa an cire shugabannin ‘yan adawa daga zaben, masu lura da al’amura sun yi imanin cewa shugaban da ke kan mulki ba tantama zai iya lashe zaben.
A ranar Asabar da yamma, shugaban hukumar zaben kasar mai zaman Kanta ya nuna cewa yawan wadanda suka fito a zagaye na farko “zai kai kusan kashi 50%.
Za a kuma sanar da sakamakon ne zuwa ranar Litinin, 27 ga watan Oktoba.