‘Yan Hamayyar Tanzaniya Sun Ki Amincewa Da Hana Su Shiga Zabe

Jam’iyyar Hamayyar siyasa ta “Chadema” a kasar Tanzania ta ki amincewa da matakin gwamnatin kasar na haramta mata shiga manyan zabukan da za a yi

Jam’iyyar Hamayyar siyasa ta “Chadema” a kasar Tanzania ta ki amincewa da matakin gwamnatin kasar na haramta mata shiga manyan zabukan da za a yi a watan Oktoba.

Hukumar zaben kasar ta Tanzania ta zargi jam’iyyar Chameda’ da cewa ta ki amincewa ta rattaba hannu akan dokokin zabe, tana mai yin kira gare ta da ta girmama hukumar zaben kasar.

A ranar Asabar din da ta gabata ne dai babbar jam’iyyar adawa ta kasar Tanzania ta kauracewa halartar taron da aka yi wanda ya kunshi dukkanin jam’iyyun siyasa da su ka rattaba hannu akan dokokin zabe. Rattaba hannu akan dokokin dai yana a matsayin daya daga cikin sharuddan shiga cikin zabe da jam’iyyu za su yi,kamar yadda Ramadhani Kalima, daraktan hukumar zaben kasar ya fada wa manema labaru.

Sai dai kuma sakataren jam’iyyar Chadema  Regemeleza Nshala  ya bayyana matakin na  hukumar zaben da cewa ya saba wa doka. Haka nan kuma ya kara da cewa,abinda doka ta ce, duk jam’iyyar da ba ta rattaba hannu akan dokoki za a ci tararshi, ba hana shi shiga zabe ba.

An kama shugaban jam’iyyar ta Chameda,Tundu Lissu a yayin da ya shiga cikin zanga-zangar da take yin kira da a sauya dokokin zabe kafin lokacin zaben ya zo.

Jami’an ‘yan sanda sun yi awon gaba da shugaban jam’iyyar ta adawa, an kuma zarge shi da cin amanar kasa.

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun zargi gwamnatin kasar ta Tanzania da amfani da dabaru mabanbanta  na cutar da jam’iyyar ta jam’iyyar adawa. Gwamnatin kasar ta Tanzania ta yi watsi da zargin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments